Fasto Elijah Ya Aike Da Muhimmin Gargadi Ga Peter Obi Kan Shari'ar Zabem Shugaban Kasa

Publish date: 2024-08-09

Jihar Legas - A yayin da ƴan Najeriya ke zaman jiran hukuncin kotun sauraren ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, David Elijah, shugaban cocin Glorious Mount of Possibility Church, ya gargaɗi Peter Obi.

Fasto David ya gargaɗi ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar Labour Party (LP) da ya yi taka tsan-tsan da wasu na kusa da shi da masu goyon bayansa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Halin da Hamɓararren Shugaban Ƙasar Gabon Ke Ciki Ya Bayyana, Ya Aike da Saƙo Mai Muhimmanci

A yayin da yake magana a gidan talbijin na Possibility TV, Fasto Elijah ya bayyana cewa wasu daga cikin masu ƙaryar suna goyon bayan Peter Obi, ba za su iya cigaba da riƙe ɗan fatan da ya rage musu ba.

"Ka yi taka tsan-tsan", Elijah ya gayawa Obi

Idan za a iya tunawa dai Peter Obi, ɗan takarar jam'iyyar LP wanda ya zo na uku a zaɓen shugaban ƙasa, ya yi fatali da sakamakon zaɓen wanda ya bayyana Bola Ahmed a matsayin shugaban ƙasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rashin gamsuwa da sakamakon zaɓen ya sanya ɗan takarar garzaya wa kotu domin ƙalubalantar nasarar Shugaba Tinubu.

A yayin da ake zaman jiran hukuncin da kotun za ta yanke, magoya bayan Peter Obi na ganin cewa ɗan takararsu ka iya yin nasara.

Kara karanta wannan

Atiku, Obi vs Tinubu: Fitaccen Malamin Addini Ya Bayyana Yadda Shari'ar Za Ta Kare

Fasto Elijah ya bayyana cewa:

"Ka yi taka tsan-tsan ka da ka faɗa hannun mutanen da za su yaudare ka.""Akwai mutanen da za su yaudare ka, waɗanda za su ce maka za ka yi nasara, nasara ta ka ce da sauransu.""Amma ana samun saɓanin hakan, ba su da abin da za su iya yi maka. Ƙarfinsu zai ƙara, za su juya maka baya. Sai ka yi taka tsan-tsan sosai."

Wike Ya Sake Takalar PDP Fada

A wani labarin kuma, ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya sake tsokanar jam'iyyar PDP faɗa.

Tsohon gwamnan na jihar Rivers, ya ƙalubalanci shugabannin jam'iyyar da idn sun isa su dakatar da shi ko ɗauki matakin ladabtarwa a kansa.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoJ2fZZwbWaekajBsHnEpaCjmZhixqJ5wKKinmWUlnquwceipKahnmK0or7GmpuiZZeWerGx056pZqeSnnqsrc1mqqGZop6us3nZmpmepV2otbazwJuYp2WblsCiew%3D%3D